Saturday, 28 February 2015

JIRGIN SAMA MAI AIKI DA HASKEN RANA

Jirgin farko da aka kera wanda ke
amfani da hasken rana zai fara
zagayen nahiyoyin duniya.
Jirgin dai zai tashi a watan Maris
kuma za dauki tsawon watanni 5
yana zagaya duniya, wanda shi ne
irinsa na farko a cikin tarihi.
An yi gwajin jirgin daga Spain zuwa
Morocco, da kuma daga San
Francisco zuwa New York.
Jirgin da aka kera a kasar
Switzerland zai fara tashi daga kasar
Hadaddiyar Daular Larabawa a
watan Maris.
Zagayen da jirgin zai yi wanda
matukan Switzerland za su ja zai
dauki tsawon watannin 5.
Ana kallon wannan a matsayin wani
mataki da zai rage gurbatar yanayi.

No comments: