A yanzu kana iya sa wayarka
da ake kira “China Phone” ta
yi maka browsing ta hanyar
amfani da kowanne ɗaya
daga cikin layukan sadarwa
na Nijeriya wato MTN, GLO,
AIRTEL, ko kuma ETISALAT.
Nigeria tafi fice a cikin
ƙasashen dake amfani da
wayoyin salula ƙirar China.
Kana iya cewa ma mafi
yawan kayayyakin da ake
amfani da su ƙirar China a
wannan ƙasar tamu babu
kamar wayar hannu ta
salula. Sauƙin su da kuma
samun a kowanne saƙo da
lungunan kasuwanni ya sa
suka samu karɓuwa A yawan
lokaci mafi akasarin mutane
na son sayan wayoyi ƙirar
China ne saboda kyawunsu
da daɗin ko sauƙin sha’anin
su. Hakan ya sa ma har suke
iya gogayya da sauran
kamfononin waya kamar su
Nokia, Samsung, LG da dai
sauransu. Kai hatta wayoyin
dake da ake kira da komai da
ruwanki (smart phone)
kamar su Blackberry, iphones
da kuma Andriod su kansu
ba ƙaramin gogayya suke
fuskanta ba daga wayoyi
ƙirar China. Kamar yadda
aka sani ne cikin kowane da
daɗi akwai rashin sa. Domin
wani abin takaici da
waɗannan wayoyin shi ne
yadda kamfononin sadarwan
mu ba sa iya turo maka da
tsarin shiga
intanet’ (Automatic Settings)
kai tsaye kamar yadda suke
turo wa wayoyi saɓaninsu.
Duk wayar da ba ta da GPRS
to fa ba ta iya shiga Intanet,
domin ba ka da damar kaima
ka iya yin bincike da kuma
ninƙaya a sarari na Intanet.
Shiga cikin irin wannan
matsalar ya sa ni bincike har
na gano yadda ake iya canza
wannan tsarin: 1. Shiga
“menu” sannan ka hau”
Service/Intanet access” 2. Ka
taɓa “service/Intanet Access”
sannan ka zaɓi “wap
Browser” 3. Buɗe ‘Wap
browser’ sai kuma ka shiga
“settings” 4. Buɗe “Edit
profile” sai ka zaɓi wanda
kake so 5. Zaɓi “Edit profile”
sai ka shigar da ɗaya daga
cikin bayanan da za mu jero
a ƙasa wanda ya yi daidai da
layin wayarka. Homepage:
MTN: GLO: AIRTEL:
Wap.ng.airtel.com@
ETISALAT:
Wap.etisalat.com.ng@ 6. Sai
ka shiga “Data Account” ka
zaɓi wanda kake so misali
China Mobile GPRS 7. Wajen
da ake rubuta “Connection
type” sai ka rubuta “WAP 8.
WAJEN “Proxy/IP Address sai
ka zaɓi irin layinka ka rubuta
waɗannan lambobi kamar
haka: MTN: 010.199.212.002
AIRTEL: 072.018.254.002
GLO: 190.129.010.245
ETISALAT:072.055.142.251 9.
Sai wajen da aka rubuta
“Security” sai ka sa “off” 10.
Username: Wap. Password:
Wap (idan ka gama sai ka
danna “yes” sannan kai
amfani da hanyar fita ta baya
“back button”) ka fita. 11. Ka
buɗe “Data Account” ka zaɓi
“GPRS” 12. Ka buɗe “Data
Account” ka zaɓi, zaɓin ka na
shida a sama. 13. Sai gyara
‘account’ ɗin ka kamar haka:
APN: MTN:
web.gprs.mtnnigeria.net
GLO: wap.gloworld.com
AIRTEL: wap.ng .airtel.com
ETISALAT:
wap.etisalat.com.ng 14.
Wajen “Username” sai ka
rubuta “ wap. Password:
shima ka rubuta wap. Kana
kammala wa sai ka fito da ga
wajen. Ina mai tabbatar
maka cewa kana yin haka to
wayarka ƙirar China ka za ta
fara aiki wato browsing. Idan
ka gwada ya yi to sai ka
samma abokai da suke da
irin waɗannan wayoyin
kuma suna sha’awar su shiga
wannan tsarin, amma basu
san yadda ake yi ba.
Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Monday, 9 February 2015
YADDA AKE SA WAYA CHINA TAYI BROWSING
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment