Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Thursday, 12 February 2015
Dalilin Da Ya Sa Na Bai Wa Janar Buhari Gudummawar Naira Milyan Daya – Tsohuwa ’Yar Shekara 95
Rariya
RAHOTO:
Dalilin Da Ya Sa Na Bai Wa Janar Buhari Gudummawar Naira Milyan Daya – Tsohuwa ’Yar Shekara 95
Daga Aliyu Ahmad
A yayin da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya je yakin neman zabe a jihar Kebbi, ya ga jama’a babu adadi. Dubban jama’a da suka hada da matan aure da yara sun fito kwansu da kwarkwatarsu har kusan tsawon awanni sha uku suna jiran isowar Janar Muhammadu Buhari. Jama’ar sun yi cincirindo ne a filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da ke Ambursa, inda daga nan suka yi dafifi zuwa filin da aka gudanar da taron, wato filin kwallon kafa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.
Tabbas za a iya cewa al’ummar jihar Kebbi sun nuna wa Janar Muhammadu Buhari kauna a fili, inda a yayin gudanar da taron har da wasu mutane sama da dari biyar da suka zo wurin taron a kan jakuna sai kuma kungiyoyin mafarauta, masunta da na ‘yan kasuwa wadanda suka yi tafiyar sama da kilo mita talatin da biyar a kafa, wato tun daga garin Jega har zuwa Birnin Kebbi don ganin sun yi ido hudu da dan takarar shugaban kasan, wanda kaunarsa ta mamaye zukatan akasarin al’ummar Nijeriya.
Babban abin da ya fi jan hankalin jama’a a wurin taron shine, wata tsohuwa mai shekaru 95 mai suna Hajiya Fati Koko, wadda aka sani da Mai Talle Tara, wadda ta dauki kimanin awanni tara tana jiran isowar Janar Buhari don ta jaddada masa goyon bayan da take yi masa.
Baya ga wannan kauna da Hajiya Fati, wadda ‘yar kasuwa ce da ke zaune a garin Koko a karamar hukumar Koko a jihar ta Kebbi, ta kuma baiwa Janar Buhari gudummawar zunzurutun kudi har naira milyan daya daga cikin kudaden da take kasuwanci, domin ya ci gaba da gudanar da yakin neman zabensa. Wannan gudummawar ba ya daga cikin na milyoyin kudaden da ta yi don ganin jam’iyyar APC ta samu karbuwa a jihar Kebbi.
A yayin da manema labarai suka yi tattaki don jin ta bakin Hajiya Fati don jin dalilin ba da wannan gudummawar da ta yi, manema labaran sun tarar da ita tana ta faman gudanar da ayyukan girgr-girke a shagon da take sayar da abinci a garin Koko, inda ta bayyana dalilin da ya sa ta dauki tsawon awanni a filin jirgi ta na jiran isowar Janar Buhari duk da cewa shekarunta sun ja da kuma dalilin da ya sa ta ba da gudummawar wannan kudi.
Kamar yadda Hajiya Fati ta bayyana, kaunar da take yi wa Janar Buharin, wanda ta dauke shi a matsayin mutum mai gaskiya da tsoron Allah, ya samo asali ne tun daga 1983 a lokacin da ya zama shugaban kasa na mulkin soja. Ta kuma kara da cewa ta soma samun na rufin asiri ne sakamakon yadda Buhari yake da gaskiya da adalci, wanda sauran shugabannin Nijeriya suka rasa.
Kamar yadda ta ce “ ni ‘yar kwangila ce a wannan lokacin. A lokacin da Buhari ya hau mulki, na yi kwangilar gina wata makaranta a garin Gummi, wadda a yanzu take jihar Zamfara, har na naira dubu arba’in. Amma sai gwamnatin jihar Sokoto a lokacin ta ki biya na kudin. Na yi ta karbar basussuka a wurin mutane don ganin na kammala kwangilar. Amma a karkashin mulkin Buhari, sai aka kafa wani kwamiti, wanda bayan an kammala bincike sai aka biya ni kudin ba tare da bata lokaci ba. Na gina ajujuwa biyu, amma da yake gwamnatin ba ta son biyana, sai ta zarge ni da hada baki da injiniyan wajen yin algus a aikin. Amma kamar yadda na ce, kwamitin da Buhari ya kafa sun zo sun wanke aikin da na yi a matsayin ingantacce, kuma aka biya ni nan take”.
Hajiya Fati ta kuma kara da cewa a lokacin mulkin Buhari gaskiya da adalci sun yi tasiri. Domin daya daga cikin kwamitin da Buhari ya kafa ya daddaki ginin da aka ba ta kwangilar, amma bai nuna wata alamar fashewa ba, inda aka jinjina mata.
“Ina ganin mutuncin Buhari saboda gaskiya da rikon amanarsa, don haka ne ma nake mafarkin ya sake mulkar Nijeriya, inda za a kau da cin hanci da rashawa a dawo da doka da oda. Sannan kuma ba wannan karo na fara kaunarsa ba, domin ina biye da shi tun a jam’iyyun ANPP, CPC har zuwa APC. Ni da dana marigayi Lawali mun sha taka muhimmiyar rawa da suka hada da gudummawar kudi don ganin Janar Buhari ya samu nasara a zabe. A lokacin da aka ce ya fadi a zaben 2011 a karkashin jam’iyyar ANPP, na kudiri aniyar kauracewa harkokin siyasa, amma duk lokacin da na ji an sake ambaton sunan Janar Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa, sai na sake tsoma kaina a harkar siyasa don ganin an kawo sauyi a Nijeriya. Na yi matukar yin ammana da Janar Buhari bisa gaskiya da adalcin da yake da shi”, inji Hajiya Fati.
Bincike ya nuna cewa, baya ga gudummawar kudin da ta baiwa Janar Buhari don yakin neman zabe, ta kuma taka rawar ganin wajen jawo hankalin magoya bayan PDP zuwa APC a jihar Kebbi.
Wannan tsohuwa dai ta yi matukar samun karbuwa a filin jirgin, a yayin da gwamna Wamakko na jihar Sokoto ya mika mata gaisuwa kuma ya jagorance ta zuwa ga Janar Buhari bayan ya iso wurin taron. Baya ga haka kuma, shi ma kansa Janar Buharin ya wuce kai tsaye ya mika mata gaisuwa bayan ya sauka a filin jirgin. Sannan kuma bincike ya nuna cewa Hajiya Fati ba ta cazar koda sisin kobo a duk dawainiyar da take yi wa jam’iyyar APC a yankin Koko.
Ita dai wannan tsohuwa sananniya ce a garin Koko kan sana’ar abincin da take yi. Kamar yadda ta ce, ta soma sana’ar sayar da abinci ne shekaru ashirin da suka gabata, amma kafin nan tana harkokin kasuwanci tare da marigayi danta, daga bisani kuma ta shiga harkar sayar da abinci. Sannan kuma kamar yadda ta ce tana da yara sha biyar da jikoki da dama. Kuma idan ka ganta za ka yi tsammanin ba ta kai wadannan shekaru ba, kasancewar har yanzu da kwarinta. by @UC Browser
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment