SAUKO DA PAID ANDROID
APPLICATION KYAUTA
ANDROID PHONES APPLICATION
Android da IOS sune shahararrun
Operating System "OS" a kasuwar
smartphones ayau. Android da IOS
suna gogayya da junansu akasuwar
smartphones, amma daga wasa
yan watanni Android ta wuce
gaba, saboda ta samu karbuwa a
kasuwar duniya, inda ta kere
sa'arta IOS fintinkau. Kuma
shaharrun kamfanoni masu kera
smartphones kamar Samsung,LG,
HTC da Sony suna amfani da
Android OS ne. Bugu da kari,
sannan da kulawar google da
kansa, akan wadannan wayoyi.
Acikin google search ko play store
da market place Android tana
dauke da duk wani application da
me amfani da ita yake bukata,
sannan akwai applications na
Android fiye da 600,000 acikin
kasuwanninta na google play store
da sauransu.
Wasu application da android take
dauka daga cikin play store
kyautane, amma kuma wasu daga
ciki saika saya, ta hanyar yin
amfani da Master card ko Visa
card ds.
To amma duk mai amfani da
wannan waya yana ganin wani
application da yake bukata, amma
kuma sai'ace maka saika biya
kudi, to ga hanyar da zaka bi ka
dauko wadannan applications
kyauta akan android naka cikin
sauki.
SAUKO DA PAID ANDROID
APPLICATION KYAUTA
Masu amfani da wayar Android
sun san akwai wasu applications,
da suke son su sauko dasu kan
wayarsu amma kuma sai'a ce sai
sun biya kudi, kuma ga shi yana
cikin play stor ko Market place,
amma kuma saika biya kudi.
Wannan dama ce zata baka damar,
sauko da duk wani application da
kake so, amma kuma akace saika
biya kudi, to bi wannan matakin
ka dauko shi kyauta.
HANYA TA FARKO
Idan kana bukatar sauko da paid
applications saika ziyarci daya
daga cikin wadannan webs din,
domin duk applications da suke
wannan shafin na masu amfani da
android ne,
www.4shared.com ,
www.mediafire.com da
www.filecrop.com .
Misali idan ka dubo sunan
application a play store, saika
ziyarci daya daga wadannan
shafuka ka sauko da shi, misali
zaka dauko Duniyarcomputer ex
application, amma kuma saika
biya kudi, to saika ziyarci daya
daga cikin wadancan shafukan ka
rubuta "Duniyar Computer ex.apk"
zai zo kan wayanka kyauta, haka
zaka kara aduk paid applications
wato ka kara ".apk" zaizo kyauta.
HANYA TA BIYU
1. Sauko da "Blackmart Alpha"
application acikin wayarka
android, wanda shi zaibaka damar
sauko da application ta cikinsa.
2. Ka ziyarci, gallery.mobile9.com/
f/2134454/ domin sauko da
"Blackmart Alpha" application
acikin wayarka android.
3. Kayi Install nasa acikin Android
Phone.
4. Ka bude Google Play
Store saika binciko sunan paid
application din da kake son sauko
da shi.
5. Idan ka binciko shi, saika dauko
sunan paid application din, saika
bude "Blackmart Alpha" ka binciko
sunan wannan application din da
ka dauko sunansa a google play
store.
6. Bayan ka binciko sunan saika
latsa download, bayan ya zo kayi
install nasa.
Ta wannan hanya zaka sauko da
duk wani paid application akan
android.
1 comment:
Hardakarama tanayi
Post a Comment