Thursday, 12 February 2015

YADDA AKE BUDE LITTAFI A WAYA

Wannan wata damace da zataba
mai koyo damar koyon hada
litafi da kanshi, domin
raraba shi ga 'yan uwa da
abokai.
Ko dai ta hanyar yin upload a
site ayi downloading ko kuma ta
hanyar turawa ta Bluetooth.
ABUBUWAN DA AKE BUKATA
WAJEN HADA LITTAFIN SUNE....
1. BlueFTP
2. Class Editor
dan haka idan ka tabbata ka
mallake su, to saika bi
wadannan matakan nakasa.
Ka sami file kamar Hoto wanda
nauyinsa bai wuce 10KB.
Yanzu sai ka bude Class Editor
dinka zaka ga ya nuno ma /E://
da kuma /C:// wanda
suke nufin idan file din da
zakayi amfani dashi a kan
memory dinka yake to se ka
zabi /E:// ko kuma /C:// idan a
kan waya
yake, idan kaje kan file din sai
ka danna Ok ka budeshi,
Zakaga ya kawo maka
wasurubutuka barkatai.
Sai ka danna *, zai fara marking,
sai kaita danna Kasa/down key,
har sai kayi marking duka page
din gaba daya.
Sai ka danna 5 sannan ka danna
6 sau uku.
Daganan zakaga page din ya
zama babu komai.
sai ka danna 5, zakaga options
kamar haka hexdec
Da dai sauransu, sai ka danna
wajen text din, to a nan se ka
fara rubutun abin da zaka rubuta
a littafin naka, a nan yana
daukan character ko harufa 1000
a java,
symbian kuma 4000, in ka gama
rubutun sai ka danna option
zakaga ok, sai ka
dannashi, kada ka kuskura ka
danna ok na navigation key, in
ba haka ba zaka goge
duk abinda karubuta.
Amma idan da waya java zakai
aikin to ana kara harufan
rubutun dan haka idan kana
bukatar harrufan su zarce 1000
to saika kara danna 5, zakaga
add text to saika kara ta nan.
Bayan ka gama rubutun sai ka
shiga option zakaga save save as
option.
Sai ka zabi save din, sai kai ta
danna yes har sai yasa over
write,
to sai ka fita daga Class Editor
dinka.
Daga nan Sai ka Bude BlueFTP
din ka sai kaje foldar da file
dinka yake san nan ka je
kan file din, ka danna option,
sai kazabi rename item.
Anan se ka goge sunan file din
kasa sunan da kake son sama
littafin misali: Hadith to
amma dolene duk sunan da kasa
karshen sa ya zama ka sa .txt in
ba haka ba to bazaiyiba.
Shike nan littafinka ya hadu sai
ka fita daga BlueFTP dinka kaje
kan wayar ka ka bude
file din zakaga yazama littafi..
Ina fata zaku riqi wannan
hanyar domin samar ma kanku
da littatafai naku na kanku
acikin wayoyinku, da kuma
adana wasu baya nai da akasan
za'aci moriyar su anan gaba

No comments: