Android wacce ake furta ta
da Hausa anduroyid manhaja
(OS) ce da kamfanin Google
Media Inc da ke kasar
Amurka ya mallaki lasisinsa
wanda shi wannan manhajar
ake amfani da ita a kan
wayoyin hannu da kuma
ƙananan kwamfutocin hannu
da ake kira da Table PC.
Su irin wannan wayoyi na
Android ba kamar sauran
waya ba ce kasancewar ita
tsarin riƙe ta da tsarin
amfani da ita ba a ko’ina ake
yi ba. Shi ya sa na ga ya dace
in yi mana bayanai a kan
waɗansu tambayoyi guda
bakwai da ya kamata mai
amfani da waɗannan wayoyi
ya sani kuma ya san yadda
zai amfani da ita.
1) Dole ne sai na yi amfani
da Google Accout kafin in
iya amfani da Android?
Haka yake! Dole duk wanda
ya sayi waya ko kuma tablet
ya zama yana da account tare
da kamfanin google kafin ya
yi amfani da ita. Amma
wannan ba yakebance cewa
akwai wani ɓangare na
google accout wanda ya zama
wajibi ne a ce shi ne mutum
zai yi amfani da shi ba. Abin
da ake so kawai ka yi rajista
da kamfanin ta wurin
mallakar ɗaya daga cikin
abubuwan da suke gabatarwa
na ayyukansu, kamar gmail
da makamantansu. Kodayake
google yana ba mutum damar
kara wani imel wanda ba
google ba, sai dai duk lokacin
da mutum yake son ya shiga
ya ƙara wa wayar tashi ko
tablet dinshi kuzari ko kuma
ya kara mata wani
application, to dole sai in
yana da account tare da
google. Kuma akwai waɗansu
abubuwa masu matukar
amfani ga mai amfani da
wayar android ko tablet
wanda idan mutum ba ya
amfani da account na google
ba ne, to ba zai same su ba.
2) Wace hanya ce ta fi kyau
wacce zan bi in kwashe duk
sunayen da suke cikin
wayata?
Akwai hanyoyin da mutum
zai iya bi domin ya ga ya
kwafe tsofaffin lambobin
cikin wayarsa zuwa wayarsa
ta android. Ɗaya daga cikin
hanyar shi ne mutum zai iya
buɗe google sai ya shiga
dakin aikawa da sakon imel
wanda ake kira da gmail, to
sai ya rubuce dukkanin
sunayen da ke wayarsa daga
nan lambobin da kansu za su
dawo cikin wayarsa ko kuma
tablet pc ɗin shi. Ko kuma ka
yi amfani da tsohuwar hanya
na kwafe lambobinka a cikin
SIM ɗinka sannan ka saka shi
cikin wayar android ko tablet
sannan ka kwafe shi cikin ta.
3) Mene ne dalilin da ya sa
wayoyin android ba sa
kama da juna?
Kamfanin google su suka
kirkiri manhajan Android
amma kuma sai suka bai wa
kamfanonin da suke yin
waya damar su yi amfani da
wannan manhajar a cikin
wayoyinsu. Saboda haka shi
ya sa kake ganin fuskokin da
kuma kamanninsu ya
banbanta. Kamfanonin da
suke da wannan lasisi sun
haɗa da kamfanin Samsung
da kuma kamfanin HTC,
wanda waɗannan
kamfanonin kowannensu,
kera waya da kuma kayan
Kwamfuta yake yi. Saboda
haka kowane ɗaya daga
cikinsu yana da damar ya yi
irin kalar waya ko kuma
tablet da yake ganin za ta
amsu a hannun abokanen
cinikinsa.
4) To yaya za a yi in samu
android wacce ba ta
waɗancan kamfanonin ba?
Idan baka son ɗaya daga
cikin wayoyin da kamfanin
HTC ko Samsung suke yi, to
ai kamfanin google yana da
tashi wayar mai suna NEXUS.
Wanda aka fi sani da Nexus
7 Tablet da kuma Galaxy
Nexus Phone. Waɗannan
guda biyu da manhajar da
kuma karafan da suke jikinsu
duk mallakar kamfanin
google ne. Sannan kuma su
waɗannan wayoyi ko da
wane lokaci kamfanin google
yana ƙoƙarin inganta su ta
wajen manhajin da suke
amfani da su, kasancewar
suna samun komai kai tsaye
daga wurin google. Su kuwa
sauran wayoyi kamar na HTC
da Samsung waɗanda suke
amfani da manhajar android
sukan ɗauko wani lokaci mai
tsawo kafin a waiwayi
manhajar tasu, domin abu ne
mai yawa da kuma faɗi da
kuma abubuwan da
waɗancan kamfanonin suke
yi yana musu yawa.
5) Mene ne banbanci
tsakanin Home Screen da
kuma App Drawer?
Shi App Drawer shi ne
wurin da za ka samu
dukkanin application da ka
ɗaura wa android, an kira
wurin da Drawer kamar
yadda malam Bahaushe ya
sani da matsayin rumbu
kasancewar nan ne ake
samun abubuwan da aka
ajiye a ciki. Saboda haka
Adroid suna da fallaye guda
bakwai da suka baka damar
ka fito da dukkanin
application da kake yawan
aiki da su, domin samun
sauƙi. To, waɗannan
application da ka saka a kan
wannan falle shi ake kira da
Home Screen. Su kuma
application da baka son
ganinsu a wannan fallen su
kuma suna cikin App
Drawer.
6) Mene ne Widgets?
Widget kamar yadda ake
furta su da Hauwa “wijet”
suna da amfani matuka
domin su ana amfani da su
wajen bayar da waɗan su
bayanai da kuma tattalin
wutar batirin android. Su
kamar hotuna ne na waɗansu
application da ka saka a
cikin Home Screen ɗin ka
wanda za su riƙa faɗa maka
abubuwan da yake gudana
ƙarƙashin waɗannan
application da ka saka su a
cikin wijet ɗin. Misali wanda
ya ɗauko application na
facebook ko twitter ko na
gmail ya saka a cikin wijet to
duk sakon da ya shigo, ɗaya
daga cikin waɗannan
application ɗin zai ga
matashiya kai tsaye wanda
ba sai ya buɗe shi application
karan kansa ba.
7) Ina da abubuwan
saurare a itunes zan iya
sauraronsu a android dina?
Akwai wani software da ake
kira da doubleTwist yana aiki
kamar yadda ka san Itunes
yake yi. Saboda haka idan ka
ɗaura shi zai baka damar
saukar da duk abin da kake
da su a Itunes zuwa Android
ɗinka.
Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Saturday, 14 February 2015
ABUBUWA MASU MAHIMMANCI GAMAI ANDROID YAKAMATA YA SANI
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment