Wikileaks da suka fitar da bayanan
sirri na diplomasiyyar Amirka a
shekarar 2010 sun sake fitar da wasu
sabbin bayanan.
Da yawa daga cikin bayanan masu
shafi dubu 60 na magana ne game
da kasar Saudiyya.
Haka zalika, daga cikin abubuwanda
suka fi jan hankali a bayanan shi ne
na cewa Amirka ta bayar da dala
biliyan 10 ga gwamnatin Masar don
ta saki hambararren shugaban kasar
Husni Mubarak.
Ana hasashen cewa wadannan
takardu sun shafi batutuwan shekarar
2012 ne.
Wani batu mai muhimmanci dake
cikin takardun kuma shi ne na game
da dan shugaban kungiyar Alqa'ida
Usama Bin laden wato Abdallah Bin
Laden, cewa ya nemi Amirka da ta ba
shi shaidar cewa mahaifinsa ya
mutu.
Amma a wasikar amsa da jakadan
Amirka a birnin Riyadh ya aike ya
bayyana cewa, ba a bayar da
takardun shaidar mutuwar wadanda
aka kashe a farmakin da aka kaiwa
Usama ba, amma kuma wata kotu a
Amirka ta aike da shaidar mutuwar
tasa.
Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya
kuma ta ce ba za ta karyata takardun
ba, amma kuma ta yi gargadin kar a
bawa 'yan kasarta takardu na bogi.
Wikileaks sun bayyana cewa a
makwanni masu zuwa za su fitar da
bayanai masu shafuka dubu dari
biyar.
Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Sunday, 21 June 2015
TRT
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment