MATASA A DAINA SHAN GANYE.
(Zainab ta saye samarin Kano)
Jiya Mutanen Sharada kwanar
Freedom sun ga abin mamaki don
kuwa tun karfe tara na safe dimbin
matasa ke tururuwa zuwa Freedom
Radio don Amsa kiran wannan matar
da kuke ganin hoton ta.
Ita dai Zainab Abdulmalik 'yar asalin
Jihar Osun ce da ke gudanar da
kasuwanci a kasuwar singa da ke
cikin kwaryar Kano ta zo freedom
radio filin IN DA RANKA tayi tayin
gida da mota kirar Honda Anaconda
ga duk wani saurayin da bai wuce
shekara 17-25 ba matukar dai zai
aure ta.
Gyatumar wadda tayi karyar
shekarunta 22 to amman ni dai ta
wakar DANGOMA
"yara suna ganin yarinya ce,
A d'ari sauranta biyar jikarta ta zarce
saba'in,
Duk wani shafe shafe mun san
tsufa.........."Inji DANGOMA .
Amman saboda da rashin aikin yi
haka matasa 'yan kwalisa na cikin
birnin Kano suka wuni suna
karakaina a bakin freedom da sun
hango mace a mota sai suyi CA akan
ta suna tambayar ko itace Zainab
karshe dai ta bayyana da misalin
karfe d'aya na rana in da matasan su
kai ta turereniya akan ta. Kamar dai
yadda nayo muku guzuri a wannan
hotunan.
Duba da kyau ki gani ko akwai
saurayin ki cikin su?
Muna rokon Allah Ya ba Matasa aikin
yi su rabu da wannan masifa ta
zaman kashe wando. — with Lawal
Ali Reseacher
Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Thursday, 18 June 2015
Abin mamaki baya qarewa
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment