Matatun man fetur guda hudu a
tarayyar Nigeria zasu dawo aiki a
cikin wata Yuli mai zuwa.
Ogi Alegbe kakakin kamfanin man
fetur na kasar NNPC shi ne shaidawa
kamfanin dillancin labarai na AFP
haka. Ya kuma kara da cewa an fara
gyarar matatun guda hudu tun da
dadewa kuma a halin yanzu an kusa
kammalawa.
Matatun man guda hudu su ne biyu a
birnin Portharcort daya a Warri sai
kuma guda a birnin Kaduna daga
arewacin kasar. Matatun gaba daya
suna iya samar da tataccen man
fetur ganga 445,000 a ko wace rana
idan sun fara aiki.
Alegbe, ya ce karancin man da ake
fama da shi a kasar zai ragu sosai
idan matatun sun dawo aiki.
Tarayyar Nigeria dai tana samar da
danyen man fetur ganga miliyon biyu
a ko wace rana, amma tana saidasu
gaba daya zuwa kasashen wajen don
rashin aikin matatun man kasar,
sannan kuma ta sake shigo da
tataccen man da farashin
kasuwannin duniya don amfani da
shi a cikin gida.
Matatun man guda hudu dai suna
hade da depo depo na tataccen mai
masu yawa a duk fadin kasar ta
hanyar bututai.
Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Friday, 19 June 2015
Matatar man najeriya zata fara aiki
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment