HAJIYA AISHAT ALUBANKUDI, Mace
ce irin wacce Hausawa ke cewa
‘Kallabi tsakanin rawuna’ ta yi fice
wajen yada manufofin Muhammadu
Bahari a shafin yanar gizo na
FACEBOOK, Bayerabiya ce ‘yar
Nijeriya wacce ke zaune a birnin
Landon. Wakilinmu UMAR
MOHAMMAD GOMBE ya tattauna da
ita a lokacin da ta zo bikin rantsar da
sabon shugaban kasa a ranar 29 ga
Mayun da ya gabata. Ga dai hirar
kamar haka:
Hajiya ko zaki gabatar da kan ki?
Suna na Aisha Alubankudi, ni
mutumiyar Nijeriya ce, ina zaune a
Landan na kasar Ingila, na zo
wannan gagarumin taro na rantsar
da Shugaban Kasa Muhammadu
Buhari.
Bisa ga dukkan alamu shafin sada
zumunta na yanar gizo wato
FACEBOOK ya zama tamkar ruhin
rayuwar al’umma musamman ma
matasa, a tunaninki me ya kawo
haka?
To a gaskiya mutane suna amfani da
wannan shafi ne bisa dalilai
bamambanta, wasu kila don su yi
abota da nishadi ne kawai, wasu
saboda karuwar ilmi, wasu saboda
manufofin siyasa da sauransu, misali
kamar ni ina yi saboda zumunci da
kuma musayar ra’ayi da jama’a
kasancewata ina can wata kasa
daban, ta haka ne kawai zan rika jin
cewa tamkar ina tare dasu, wani
lokaci ina samun nishadi in yi dariya,
koda yake wasu na cewa ni ma ina
sanya su yin dariyar da sauransu.
Don haka dai ya danganta bisa yadda
kowa yake kallon amfani ko tasirin
wannasn fasaha ta FACEBOOK.
Kin yi fice kusan kowa ya sanki a
wannan shafi, shin mene ne sirrin?
Gaskiya ban sani ba! Sai dai kawai
abinda zan iya cewa shine; ina da
hakuri da juriya, nakan jure
maganganun mutane ko wane iri ne,
sannan ina kokari wajen ganin na
fadi abinda ya dace, wannan yasa
idan na yi rubutu mutane ke son
karantawa, sannan kuma nakan fadi
abinda ke cikin raina kai tsaye, kila
saboda haka ne mutane ke rububina
ban sani ba.
Nawa ne yawan wadanda kika
amince da su a matsayin abokanki a
shafin?
Ba su wuce 1,000 ba.
Ya suka yi kadan haka?
E zaka iya cewa sun yi kadan, amma
akwai kusan mutune 4,000 da suka
aiko min da tayin abota amma ban
amsa ba.
Saboda me?
Akwai dalilai da dama, wadansu ba
mutanen kirki ba ne suna sanya
hotunan batsa a shafina, wasu kuma
ban san su ba saboda babu
fuskokinsa a bayyane, don haka kafin
in amshe abotar mutum sai na bibiyi
shafinsa na ga ko shi waye, kuma
wadanne irin sakonni yake isar wa ga
al’umma? Idan na ga ya san abinda
yake yi sai in amshi abotarsa.
Me ya ja hankalinki har kika fara
kamfen na neman canji a
shugabancin Nijeriya?
Na fara wannan kamfen tun a
shekarar 2011, hasalima dai na fi yin
kokari a wancan lokaci fiye da
wannan karon na 2015. Abinda yasa
kila a wancan lokaci wasu ba su sani
ba shine; Bahari ya tsaya takara da
wasu ‘yan Arewa da yawa, sannan
kuma shi kan sa Jonathan yana da
dan sauran numfashi a wancan
lokaci fiye da yanzu, akwai masu
sonsa. Amma a wannan lokaci babu
mai kaunarsa, kuma shi da Buhari ne
kawai ‘yan takarar. Amma a zahiri na
fi samun kalubale a 2011 saboda
yadda wasu suka rika yi min
barazana da kuma bakaken
maganganu da sauransu.
To yanzu ga shi canjin ya samu, kin
dawo gida Nijeriya kenan ko kuwa
dai zaki sake komawa can Ingila?
To gaskiya na jima sosai a can
Ingila, kuma idan na gaya maka zaka
yi mamaki, domin na bar gida ne
saboda wata matsala da na samu da
malamaina a jami’a, sai kawai na yi
tafiyata kasar waje.
Tun yashe kike a can?
Tun shekarar 1989 nake a Ingila har
zuwa yau, koda yake gangar jikina
tana can, amma ruhina yana nan
Nijeriya koda yaushe, sannan
dabi’una babu abinda ya canja,
gaskiya ina matukar son dawowa
gida Nijeriya, amma abinda kawai ya
tsayar dani shine, babban dana yana
karatu acan, kuma bani son in dawo
in bar shi, amma da zarar ya
kammala zan tattaro kayana da
yarana guda biyu mu dawo insha
Allah.
Hajiya wasu na ganin cewa an biyaki
kudi ne kika yi wannan kamfe a
yanar gizo, shin nawa ne aka baki?
Wallahi haramun! Allah ne shaidana,
babu wanda ya bani ko kwabo! Sai
ma dai ni da na bayar da
gudumawata wajen tara wa Buhari
kudin kamfe, wasu ma har cewa suke
wai an bani Fam 500,000, to idan na
samu irin wadannan kudi ka ganni
haka? Sannan wani abu ma shine, ni
fa ina yin Baba Buhari ne kawai ba
APC ko wani ba, kuma na fara son
shi tun ina ‘yar karama a lokacin da
yake mulkin soja, abubuwan da ya yi
na tarbiyya, kima da daraja har
yanzu suna nan a zuciyata ba zan
taba mancewa ba. Don haka ko
kadan ba don kudi nake yi ba.
Sabon Shugaban Kasa Muhammadu
Buhari ya ambaci wadannan
hanyoyin sadarwa na zamani, a
matsayinki na daya daga cikinsu, ya
kika ji a ranki?
Gaskiya na ji dadi kwarai, ba ma ni
kadai ba, kusan kowa ya yi mamakin
yadda ya fito ya yi yabo ga masu yi
masa kamfe a yanar gizo, kuma
shine shugaban kasa na farko da ya
fito ya yi haka, da wasu na ganin
kamar wasan yara ne kawai muke yi,
amma tunda Baba Buhari ya fito ya
fadi haka, yanzu mutane sun gane
muhaimmancin hakan.
La’akari da yadda kike tsara rubutu
a shafinki, wasu na cewa ke ‘yar
jarida ce, haka ne?
Gaskiya ni ba ‘yar jarida ba ce. Ni
ma’aikaciya ce a hukumar kananan
hukumomi acan Ingila, amma ba ‘yar
jarida ba kamar yadda wasu ke zato.
Ya batun aure kuma?
Me yasa kake son sani?
Saboda yadda na ga a kullum
mutane ke tambayarki a FACEBOOK,
amma baki bada amsa.
To gaskiya ba ni da aure a halin
yanzu.
Kin taba aure kenan acan baya?
E, amma an sake ni yanzu.
Ke nan a kasuwa kike?
E ina kasuwa, amma sai mai kudi
kamar Dangote zan aura… (dariya).
Hajiya kwanakin baya kin yi
barazanar cewa zaku yi zanga-
zangar mata milyan daya tsirara idan
har Sanata Aisha Jummai Alhassan
ta fadi zabe a Jihar Taraba, ina aka
kwana ne?
Dariya…. Wallahi wasa ne kawai,
haba ya za a yi haka? Ni fa Musulma
ce! Yin tsiraici ai haramun ne,
wannan kawai na fada ne don
nishadi. Kuma abin mamaki wasu
mutane sun kasa fahimtata a haka,
sau da yawa idan na yi rubutu ina
samun suka sosai, ni kuma wasu
abubuwan ina yin su ne don nishadi.
Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Tuesday, 23 June 2015
HAJIYA AISHA MACE MAI KAMAR MAZA KALLABI TSAKANIN RAWUNA
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment