Thursday, 18 June 2015

Matashiyar nan yar sheka 22 tasamu mijin aure

A ranar Laraba ne wata matashiyar
nan da ta janyo cuncurundon
daruruwan maza a jihar Kano a gidan
rediyon Freedom da ke jihar ta zabi
miji, bayan da ta yi alkawarin za ta
bayar da mota da kudi da kuma gida
ga duk wanda ya aure ta.
Wani ma'aikacin gidan rediyon
Freedom ya ce "ta zabi saurayi guda
kuma 'yan sanda sun dauke su tare
sun tafi saboda basu kariya daga
cincirindon mutane, amma sun
rabuda da ita bayan sun fitar da su.
Matashiyar, Zainab Abdulmalik mai
shekaru 22, ta bayyana aniyarta ne a
wani sannanen shiri mai suna "In da
Ranka", inda ta ce za ta bayar da
wadannan kyaututuka ga duk wanda
ya aure ta.
Matasa, wadanda suka kure adaka,
daga sassan jihar sun yi tururuwa a
ofishin gidan rediyon Freedom da ke
unguwar Sharada.
Matashiyar ta bukaci duk matashi
mai shekaru daga 17 zuwa 25 ya je
gidan rediyon domin a tantance shi a
ranar Laraba da safe.
Tun da misalin karfe 11 na safe
matasa suka fara taruwa, a inda aka
bukace su da su taru har sai da
Zainab ta iso wurin da misalin karfe
1 na rana.
Zainab Abdul, 'yar asalin jihar Osun
da ke kudu maso yammacin Najeriya,
ta ce ta yi niyyar bayar da
kyaututukan ne saboda tsohon
saurayinta wanda suka kwashe
tsawon shekaru suna tare ya yaudare
ta.
Ta ce "Ni 'yar kasuwa ce a Kasuwar
Singa kuma na kashewa tsohon
saurayi na kusan naira miliyan biyar
amma sai ya wulakanta ni duk da
wadannan abubuwan da na yi masa.
Saboda haka ne na je gidan radio
domin bayar da sanarwar
kyaututukan da zan bayar ga duk mai
so ya aure ni. Bana tare da kowa
kuma ban taba aure ba."

No comments: