Mene Ne Gaskiyar Lamarin Matar Da
Ta Sanar Da Neman Mijin Aure A
Kano?
Daga Aliyu Ahmad
A ranar Talatar da ta gabata ne wata
baiwar Allah wadda ta bayyana
sunanta a matsayin Zainab
Abdumalik, mai kimanin shekaru 22
ta fito gidan rediyon Freedom da ke
jihar Kano ta sanar a wani shiri mai
taken ‘Inda Ranka’ cewa tana bukarat
mijin aure, tare kuma da yi masa
goma ta arziki, ma’ana za ta mallaka
masa mota da gida sannan kuma zai
ci gaba da tafiyar da harkokin
kasuwancinta.
Hakan ne ya sa bayan an kammala
gudanar da shirin a daren ranar
Talatar, tun safiyar Laraba daruruwan
jama’a, musamman matasa suka yi
cincirindo a gidan rediyon domin
jarraba sa’arsu a wurin wannan
baiwar Allah da ta ce tana neman
mijin daga mai shekaru 18 zuwa 25.
Sai dai daga dukkan bayanai da
yanzu suke tabbata matar, wadda
‘yar asalin jihar Osun ce, labarin na ta
ya zama tamkar tatsuniya, domin
gamsassun hujjoji daga wadanda
suka san ta sun tabbatar da cewa
biredi ta ke sayarwa a unguwar
Jakara da ke jihar ta Kano sabanin
kasuwar Singa da ta fada. Sannan ba
ta da mota sabanin cewa da ta yi ta
na da Henesy. Ba ta kuma da damar
yin kyautar ko da rago ballantana
gida da mota da kuma Jari.
Haka kuma bincike ya nuna cewa a
lokacin da ta dawo gidan rediyon da
safe bayan ta bada sanarwar, an
gano cewa a babur mai kafa uku ta
zo wurin, wanda aka fi sani da A
Daidaita sahu.
Haka kuma bincike ya nuna cewa
batun da ta yin a cewa wani ya
yaudare ta tare da damfarar ta
miliyan biyar, shi ma karya ne. Kai
hasali ma sun tabbatar da cewa ta na
da tabin hankali. Sannan kuma
majiya mai tushe ta rawaito cewa
daya daga cikin wakilan gidan
Rediyon na Freedom ya tabbatar da
su ma sun samu wannan labarin
daga baya.
Sai dai a wani rahoto da ya biyo
baya, ya nuna cewa matashiyar ta
zabi daya daga cikin dandazon
jama’an da suka yi cincirindo a
gidan rediyon, inda jami’an tsaro
suka kwashe su biyun don gudun
kada wani abin ya same su a wuirin.
Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Friday, 19 June 2015
Rariya
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment