Tuesday, 23 June 2015

GARABASA DAGA MTN

FASAHA Maza Ka Hanzarta Morema
Mtn Happy Ramadan Free Browsing
Ina Mai Farin Cikin
Sanar Daku Cewa Kamfanin Mtn
Suna Bada Wasu Kwanaki Na
Musamman Domin Yin Browsing
Kyauta
Domin Haka Yanzunnan Kawai Ka
Tabbata Kana Tsarin Mtn Ipules Ne
Idan Baka Toka Dannan *406#
domin
komawa Sannan Ka Tabbata
Layinka Babu Ko Sisi Acikinshi
Kuma Babu Mb Sannan Kasashi
Cikin Wayarka Idankasa Karka Jira
Bata Lokaci Kawai Ka Bude bude ko
wacce kalar browser ka fara
browsing da Ita Kamar Opera min ,
uc browser , 2go , bb , whatsapp
Da Komai Duka Free Zaka Rinka
Budesu Har Zuwa Lokacinda
Wannan
Offer Zata Kare
Domin Nidai Wllh Tun Jiya Da Dare
Zuwa Yau Duka Layikana Na Mtn
Na
Gwada Free Browsing Sukeyi Kuma
Babu Wanda Yakeda Ko Sisin Kobo
Ballantana Mb Hakama Kuma
Abokaina Duka Na Fadamusu Kuma
Suma Sunayi Normal Domin Haka
Yasa Na Samu Kwarin Guiwa Da
Yakinin Kowa Zai
Iya More wannan garabasa

HAJIYA AISHA MACE MAI KAMAR MAZA KALLABI TSAKANIN RAWUNA

HAJIYA AISHAT ALUBANKUDI, Mace
ce irin wacce Hausawa ke cewa
‘Kallabi tsakanin rawuna’ ta yi fice
wajen yada manufofin Muhammadu
Bahari a shafin yanar gizo na
FACEBOOK, Bayerabiya ce ‘yar
Nijeriya wacce ke zaune a birnin
Landon. Wakilinmu UMAR
MOHAMMAD GOMBE ya tattauna da
ita a lokacin da ta zo bikin rantsar da
sabon shugaban kasa a ranar 29 ga
Mayun da ya gabata. Ga dai hirar
kamar haka:
Hajiya ko zaki gabatar da kan ki?
Suna na Aisha Alubankudi, ni
mutumiyar Nijeriya ce, ina zaune a
Landan na kasar Ingila, na zo
wannan gagarumin taro na rantsar
da Shugaban Kasa Muhammadu
Buhari.
Bisa ga dukkan alamu shafin sada
zumunta na yanar gizo wato
FACEBOOK ya zama tamkar ruhin
rayuwar al’umma musamman ma
matasa, a tunaninki me ya kawo
haka?
To a gaskiya mutane suna amfani da
wannan shafi ne bisa dalilai
bamambanta, wasu kila don su yi
abota da nishadi ne kawai, wasu
saboda karuwar ilmi, wasu saboda
manufofin siyasa da sauransu, misali
kamar ni ina yi saboda zumunci da
kuma musayar ra’ayi da jama’a
kasancewata ina can wata kasa
daban, ta haka ne kawai zan rika jin
cewa tamkar ina tare dasu, wani
lokaci ina samun nishadi in yi dariya,
koda yake wasu na cewa ni ma ina
sanya su yin dariyar da sauransu.
Don haka dai ya danganta bisa yadda
kowa yake kallon amfani ko tasirin
wannasn fasaha ta FACEBOOK.
Kin yi fice kusan kowa ya sanki a
wannan shafi, shin mene ne sirrin?
Gaskiya ban sani ba! Sai dai kawai
abinda zan iya cewa shine; ina da
hakuri da juriya, nakan jure
maganganun mutane ko wane iri ne,
sannan ina kokari wajen ganin na
fadi abinda ya dace, wannan yasa
idan na yi rubutu mutane ke son
karantawa, sannan kuma nakan fadi
abinda ke cikin raina kai tsaye, kila
saboda haka ne mutane ke rububina
ban sani ba.
Nawa ne yawan wadanda kika
amince da su a matsayin abokanki a
shafin?
Ba su wuce 1,000 ba.
Ya suka yi kadan haka?
E zaka iya cewa sun yi kadan, amma
akwai kusan mutune 4,000 da suka
aiko min da tayin abota amma ban
amsa ba.
Saboda me?
Akwai dalilai da dama, wadansu ba
mutanen kirki ba ne suna sanya
hotunan batsa a shafina, wasu kuma
ban san su ba saboda babu
fuskokinsa a bayyane, don haka kafin
in amshe abotar mutum sai na bibiyi
shafinsa na ga ko shi waye, kuma
wadanne irin sakonni yake isar wa ga
al’umma? Idan na ga ya san abinda
yake yi sai in amshi abotarsa.
Me ya ja hankalinki har kika fara
kamfen na neman canji a
shugabancin Nijeriya?
Na fara wannan kamfen tun a
shekarar 2011, hasalima dai na fi yin
kokari a wancan lokaci fiye da
wannan karon na 2015. Abinda yasa
kila a wancan lokaci wasu ba su sani
ba shine; Bahari ya tsaya takara da
wasu ‘yan Arewa da yawa, sannan
kuma shi kan sa Jonathan yana da
dan sauran numfashi a wancan
lokaci fiye da yanzu, akwai masu
sonsa. Amma a wannan lokaci babu
mai kaunarsa, kuma shi da Buhari ne
kawai ‘yan takarar. Amma a zahiri na
fi samun kalubale a 2011 saboda
yadda wasu suka rika yi min
barazana da kuma bakaken
maganganu da sauransu.
To yanzu ga shi canjin ya samu, kin
dawo gida Nijeriya kenan ko kuwa
dai zaki sake komawa can Ingila?
To gaskiya na jima sosai a can
Ingila, kuma idan na gaya maka zaka
yi mamaki, domin na bar gida ne
saboda wata matsala da na samu da
malamaina a jami’a, sai kawai na yi
tafiyata kasar waje.
Tun yashe kike a can?
Tun shekarar 1989 nake a Ingila har
zuwa yau, koda yake gangar jikina
tana can, amma ruhina yana nan
Nijeriya koda yaushe, sannan
dabi’una babu abinda ya canja,
gaskiya ina matukar son dawowa
gida Nijeriya, amma abinda kawai ya
tsayar dani shine, babban dana yana
karatu acan, kuma bani son in dawo
in bar shi, amma da zarar ya
kammala zan tattaro kayana da
yarana guda biyu mu dawo insha
Allah.
Hajiya wasu na ganin cewa an biyaki
kudi ne kika yi wannan kamfe a
yanar gizo, shin nawa ne aka baki?
Wallahi haramun! Allah ne shaidana,
babu wanda ya bani ko kwabo! Sai
ma dai ni da na bayar da
gudumawata wajen tara wa Buhari
kudin kamfe, wasu ma har cewa suke
wai an bani Fam 500,000, to idan na
samu irin wadannan kudi ka ganni
haka? Sannan wani abu ma shine, ni
fa ina yin Baba Buhari ne kawai ba
APC ko wani ba, kuma na fara son
shi tun ina ‘yar karama a lokacin da
yake mulkin soja, abubuwan da ya yi
na tarbiyya, kima da daraja har
yanzu suna nan a zuciyata ba zan
taba mancewa ba. Don haka ko
kadan ba don kudi nake yi ba.
Sabon Shugaban Kasa Muhammadu
Buhari ya ambaci wadannan
hanyoyin sadarwa na zamani, a
matsayinki na daya daga cikinsu, ya
kika ji a ranki?
Gaskiya na ji dadi kwarai, ba ma ni
kadai ba, kusan kowa ya yi mamakin
yadda ya fito ya yi yabo ga masu yi
masa kamfe a yanar gizo, kuma
shine shugaban kasa na farko da ya
fito ya yi haka, da wasu na ganin
kamar wasan yara ne kawai muke yi,
amma tunda Baba Buhari ya fito ya
fadi haka, yanzu mutane sun gane
muhaimmancin hakan.
La’akari da yadda kike tsara rubutu
a shafinki, wasu na cewa ke ‘yar
jarida ce, haka ne?
Gaskiya ni ba ‘yar jarida ba ce. Ni
ma’aikaciya ce a hukumar kananan
hukumomi acan Ingila, amma ba ‘yar
jarida ba kamar yadda wasu ke zato.
Ya batun aure kuma?
Me yasa kake son sani?
Saboda yadda na ga a kullum
mutane ke tambayarki a FACEBOOK,
amma baki bada amsa.
To gaskiya ba ni da aure a halin
yanzu.
Kin taba aure kenan acan baya?
E, amma an sake ni yanzu.
Ke nan a kasuwa kike?
E ina kasuwa, amma sai mai kudi
kamar Dangote zan aura… (dariya).
Hajiya kwanakin baya kin yi
barazanar cewa zaku yi zanga-
zangar mata milyan daya tsirara idan
har Sanata Aisha Jummai Alhassan
ta fadi zabe a Jihar Taraba, ina aka
kwana ne?
Dariya…. Wallahi wasa ne kawai,
haba ya za a yi haka? Ni fa Musulma
ce! Yin tsiraici ai haramun ne,
wannan kawai na fada ne don
nishadi. Kuma abin mamaki wasu
mutane sun kasa fahimtata a haka,
sau da yawa idan na yi rubutu ina
samun suka sosai, ni kuma wasu
abubuwan ina yin su ne don nishadi.

GET GLO 1GB FOR 100

I saw this message in my sms from
Glo saying Get it easily, 1GB for
N100 valid for 15 days! Write 1 and
reply, enter online world with this
tremendous data bundle. Glo
Unlimited!
I don’t know what their intention is
on this plan or maybe its for those
who got the text, that I can’t say but
it works.
How Can I Activate it?
==>If you wanna try it out, load 100
or more on your glo line and send 1
to 8070
==>Wait for some time and you
should get a success message like
this “Dear Customer, your 1 GB data
bundle has been successfully
activated. Enjoy it until …”
Mind you, this plan is only valid for
15days.Try it and enjoy the ride for
the evening

Monday, 22 June 2015

YADDA AKE FITA DAGA TSARUKAN MTN DA SUKE CIRE KUDI

:::MTN USERS
IDAN MTN SUNA CIRAMA KUDI
BATARE DA KASAN DALILIBA TO KA
JARRABA CANCEL NA WADANNAN
PLAN DIN:-
1= CNN Breaking News UFCNN to
700 2= CNN Breaking News
CNNBREAK STOP to 700 3= CNN
Politics CNNPOL STOP to 700 4=
CNN Business CNNBIZ to 700 5=
CNN Entertainment CNNENT to 700
6= CNN Sport CNNSPORT to 700 7=
Learn English Weekky ULEN to 700
8= BBC News STOP NEWS to 4200
9= Local News English STOP1 to
33555 10= Weather Updates OUT512
35070 11= Football Updates STOP to
4080 12= Local News Pidgin
ULNPIDGIN to 700 13= Local News
Yoruba ULNYORUBA to 700 14=
Guardian UGBN to 700 15= Forex
update UFOREX to 700 16= AFP
News UAFP to 700 NEWS & FC 1=
Chelsea FC News UCFC to 700 2=
Chelsea FC Monthly NO CFM to 4900
3= Chelsea FC Weekly NO CFW to
4900 NEWS & LIFSTYLE 1= Love
Messages CANCELLOVE to 33118 2=
Love Quotes Weekly UWLQUOTE to
700 INSPIRATION 1=Bishop T.D
Jakes Pastor Joel osteen Bible
quotes weekly Open heeavens weekly
Bible promise daily Daily DUA Daily
AYAT Daily HADITH Motivational
Quotes Dukansu Domin Cancel Ku
Aika UWMMQUOTES to 700 WORD
OF THE DAY 1= Daily Inspiration
Prayer OUTINS to 35070

Sunday, 21 June 2015

TRT

Wikileaks da suka fitar da bayanan
sirri na diplomasiyyar Amirka a
shekarar 2010 sun sake fitar da wasu
sabbin bayanan.
Da yawa daga cikin bayanan masu
shafi dubu 60 na magana ne game
da kasar Saudiyya.
Haka zalika, daga cikin abubuwanda
suka fi jan hankali a bayanan shi ne
na cewa Amirka ta bayar da dala
biliyan 10 ga gwamnatin Masar don
ta saki hambararren shugaban kasar
Husni Mubarak.
Ana hasashen cewa wadannan
takardu sun shafi batutuwan shekarar
2012 ne.
Wani batu mai muhimmanci dake
cikin takardun kuma shi ne na game
da dan shugaban kungiyar Alqa'ida
Usama Bin laden wato Abdallah Bin
Laden, cewa ya nemi Amirka da ta ba
shi shaidar cewa mahaifinsa ya
mutu.
Amma a wasikar amsa da jakadan
Amirka a birnin Riyadh ya aike ya
bayyana cewa, ba a bayar da
takardun shaidar mutuwar wadanda
aka kashe a farmakin da aka kaiwa
Usama ba, amma kuma wata kotu a
Amirka ta aike da shaidar mutuwar
tasa.
Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya
kuma ta ce ba za ta karyata takardun
ba, amma kuma ta yi gargadin kar a
bawa 'yan kasarta takardu na bogi.
Wikileaks sun bayyana cewa a
makwanni masu zuwa za su fitar da
bayanai masu shafuka dubu dari
biyar.

Friday, 19 June 2015

Rariya

Mene Ne Gaskiyar Lamarin Matar Da
Ta Sanar Da Neman Mijin Aure A
Kano?
Daga Aliyu Ahmad
A ranar Talatar da ta gabata ne wata
baiwar Allah wadda ta bayyana
sunanta a matsayin Zainab
Abdumalik, mai kimanin shekaru 22
ta fito gidan rediyon Freedom da ke
jihar Kano ta sanar a wani shiri mai
taken ‘Inda Ranka’ cewa tana bukarat
mijin aure, tare kuma da yi masa
goma ta arziki, ma’ana za ta mallaka
masa mota da gida sannan kuma zai
ci gaba da tafiyar da harkokin
kasuwancinta.
Hakan ne ya sa bayan an kammala
gudanar da shirin a daren ranar
Talatar, tun safiyar Laraba daruruwan
jama’a, musamman matasa suka yi
cincirindo a gidan rediyon domin
jarraba sa’arsu a wurin wannan
baiwar Allah da ta ce tana neman
mijin daga mai shekaru 18 zuwa 25.
Sai dai daga dukkan bayanai da
yanzu suke tabbata matar, wadda
‘yar asalin jihar Osun ce, labarin na ta
ya zama tamkar tatsuniya, domin
gamsassun hujjoji daga wadanda
suka san ta sun tabbatar da cewa
biredi ta ke sayarwa a unguwar
Jakara da ke jihar ta Kano sabanin
kasuwar Singa da ta fada. Sannan ba
ta da mota sabanin cewa da ta yi ta
na da Henesy. Ba ta kuma da damar
yin kyautar ko da rago ballantana
gida da mota da kuma Jari.
Haka kuma bincike ya nuna cewa a
lokacin da ta dawo gidan rediyon da
safe bayan ta bada sanarwar, an
gano cewa a babur mai kafa uku ta
zo wurin, wanda aka fi sani da A
Daidaita sahu.
Haka kuma bincike ya nuna cewa
batun da ta yin a cewa wani ya
yaudare ta tare da damfarar ta
miliyan biyar, shi ma karya ne. Kai
hasali ma sun tabbatar da cewa ta na
da tabin hankali. Sannan kuma
majiya mai tushe ta rawaito cewa
daya daga cikin wakilan gidan
Rediyon na Freedom ya tabbatar da
su ma sun samu wannan labarin
daga baya.
Sai dai a wani rahoto da ya biyo
baya, ya nuna cewa matashiyar ta
zabi daya daga cikin dandazon
jama’an da suka yi cincirindo a
gidan rediyon, inda jami’an tsaro
suka kwashe su biyun don gudun
kada wani abin ya same su a wuirin.

Matatar man najeriya zata fara aiki

Matatun man fetur guda hudu a
tarayyar Nigeria zasu dawo aiki a
cikin wata Yuli mai zuwa.
Ogi Alegbe kakakin kamfanin man
fetur na kasar NNPC shi ne shaidawa
kamfanin dillancin labarai na AFP
haka. Ya kuma kara da cewa an fara
gyarar matatun guda hudu tun da
dadewa kuma a halin yanzu an kusa
kammalawa.
Matatun man guda hudu su ne biyu a
birnin Portharcort daya a Warri sai
kuma guda a birnin Kaduna daga
arewacin kasar. Matatun gaba daya
suna iya samar da tataccen man
fetur ganga 445,000 a ko wace rana
idan sun fara aiki.
Alegbe, ya ce karancin man da ake
fama da shi a kasar zai ragu sosai
idan matatun sun dawo aiki.
Tarayyar Nigeria dai tana samar da
danyen man fetur ganga miliyon biyu
a ko wace rana, amma tana saidasu
gaba daya zuwa kasashen wajen don
rashin aikin matatun man kasar,
sannan kuma ta sake shigo da
tataccen man da farashin
kasuwannin duniya don amfani da
shi a cikin gida.
Matatun man guda hudu dai suna
hade da depo depo na tataccen mai
masu yawa a duk fadin kasar ta
hanyar bututai.

AIKI SAI MESHI

Buhari Ya Bada Umarnin Saida
Jiragen Fadar Shugaban Kasa Guda
Tara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
ya bada umarnin saida jiragen fadar
shugaban kasa guda tara domin rage
kudaden da Nijeriya ke kashewa ba
gaira ba dalili.
A lokacin da yake yakin neman
zabensa, Buhari ya yi alkawarin cewa
zai rage kudaden da gwamnati ke
kashewa ba tare da suna amfanar
Nijeriya.
Fadar shugaban kasa, na da jirage
16, wadanda suke lakume makudan
kudade wajen kula da su da yi musu
gyararraki.
Kafin umarnin Shugaba Buhari na
saida jirage tara, fadar shugaban
kasar Nijeriya, ita ce ke kan gaba a
nahiyar Afrika wajen yawan jiragen.

Thursday, 18 June 2015

Matashiyar nan yar sheka 22 tasamu mijin aure

A ranar Laraba ne wata matashiyar
nan da ta janyo cuncurundon
daruruwan maza a jihar Kano a gidan
rediyon Freedom da ke jihar ta zabi
miji, bayan da ta yi alkawarin za ta
bayar da mota da kudi da kuma gida
ga duk wanda ya aure ta.
Wani ma'aikacin gidan rediyon
Freedom ya ce "ta zabi saurayi guda
kuma 'yan sanda sun dauke su tare
sun tafi saboda basu kariya daga
cincirindon mutane, amma sun
rabuda da ita bayan sun fitar da su.
Matashiyar, Zainab Abdulmalik mai
shekaru 22, ta bayyana aniyarta ne a
wani sannanen shiri mai suna "In da
Ranka", inda ta ce za ta bayar da
wadannan kyaututuka ga duk wanda
ya aure ta.
Matasa, wadanda suka kure adaka,
daga sassan jihar sun yi tururuwa a
ofishin gidan rediyon Freedom da ke
unguwar Sharada.
Matashiyar ta bukaci duk matashi
mai shekaru daga 17 zuwa 25 ya je
gidan rediyon domin a tantance shi a
ranar Laraba da safe.
Tun da misalin karfe 11 na safe
matasa suka fara taruwa, a inda aka
bukace su da su taru har sai da
Zainab ta iso wurin da misalin karfe
1 na rana.
Zainab Abdul, 'yar asalin jihar Osun
da ke kudu maso yammacin Najeriya,
ta ce ta yi niyyar bayar da
kyaututukan ne saboda tsohon
saurayinta wanda suka kwashe
tsawon shekaru suna tare ya yaudare
ta.
Ta ce "Ni 'yar kasuwa ce a Kasuwar
Singa kuma na kashewa tsohon
saurayi na kusan naira miliyan biyar
amma sai ya wulakanta ni duk da
wadannan abubuwan da na yi masa.
Saboda haka ne na je gidan radio
domin bayar da sanarwar
kyaututukan da zan bayar ga duk mai
so ya aure ni. Bana tare da kowa
kuma ban taba aure ba."

Abin mamaki baya qarewa

MATASA A DAINA SHAN GANYE.
(Zainab ta saye samarin Kano)
Jiya Mutanen Sharada kwanar
Freedom sun ga abin mamaki don
kuwa tun karfe tara na safe dimbin
matasa ke tururuwa zuwa Freedom
Radio don Amsa kiran wannan matar
da kuke ganin hoton ta.
Ita dai Zainab Abdulmalik 'yar asalin
Jihar Osun ce da ke gudanar da
kasuwanci a kasuwar singa da ke
cikin kwaryar Kano ta zo freedom
radio filin IN DA RANKA tayi tayin
gida da mota kirar Honda Anaconda
ga duk wani saurayin da bai wuce
shekara 17-25 ba matukar dai zai
aure ta.
Gyatumar wadda tayi karyar
shekarunta 22 to amman ni dai ta
wakar DANGOMA
"yara suna ganin yarinya ce,
A d'ari sauranta biyar jikarta ta zarce
saba'in,
Duk wani shafe shafe mun san
tsufa.........."Inji DANGOMA .
Amman saboda da rashin aikin yi
haka matasa 'yan kwalisa na cikin
birnin Kano suka wuni suna
karakaina a bakin freedom da sun
hango mace a mota sai suyi CA akan
ta suna tambayar ko itace Zainab
karshe dai ta bayyana da misalin
karfe d'aya na rana in da matasan su
kai ta turereniya akan ta. Kamar dai
yadda nayo muku guzuri a wannan
hotunan.
Duba da kyau ki gani ko akwai
saurayin ki cikin su?
Muna rokon Allah Ya ba Matasa aikin
yi su rabu da wannan masifa ta
zaman kashe wando. —  with Lawal
Ali Reseacher

Tuesday, 16 June 2015

SABAN TSARIN EASYLIFE

Manhajar Layin Etisalat ta fito
da Wani Sabon Tsari Wanda
ake kiran shi da Easylife4.0 .
Shi dai a sabon tsarin nan da
Alama ba kamar sa a manhajar
ETISALAT, domim ana cijin kira
akan farashin 11kobo/sec
Wanda zaka iya kiran kowani
Layin dake cikin kasar Nigeria..
Idan kuma xuwa kashen waje ne
suna cajin 20k/sec Wanda duk
layin etisalat ba mai saukin shi.
Sai dai a kowace rana zasu cire
maka Naira 5 domin kiran farko
da zakayi amma duk da haka
INA ganin ba laifi tsarin akan
yanda suke da.
Taya Zan fara Amfani da
wannan Tsarin
Domin sauya Layin ka xuwa
wannan Tsarin zaka latsa
*420*1#
Sai kayi confirming ta danna
“224*3#

FREE BROWSING

Free Internet Browsing all night long
every day when you spend at least
N200 during the day! Unlimited data
available btw 1:00am-5:00am. Only
on MTN iPulse!