TATTAUNAWA: (Kashi Na Farko)
Tun Buhari Na Yaro Yake Da
Kwarjini, Cewar Yayarsa Rakiya
Adamu
HAJIYA RAKIYA ADAMU yaya ce ga
zababben shugaban kasa Janar
Muhammadu Buhari, kuma ita kadai
ce ta rage a raye cikin su ashirin da
hudu da mahaifansu suka haifa; daga
ita sai Muhammdu Buhari. A
tattaunawarsu da wakilinmu na
Katsina JAMILU DABAWA, a gidanta
da ke Kofar Baru a cikin garin Daura,
‘yar shekara saba’in da bakwai ta
bayyana masa irin halayyar Janar
Buhari da irin yadda ya yi
kuruciyarsa, karatunsa da kuma
yadda suka ji lokacin da zai tafi aikin
soja. Ga yadda hirar ta kasance:-
Hajiya za mu so jin sunanki da kuma
dangantakarki da zababben
shugaban kasa mai jiran gado?
Sunana Hajiya Rakiya Adamu. An
haife ni a nan garin Daura, kuma
uwarmu daya ubanmu daya da
Buhari, daga ni sai Buhari wato
bayan an haife ni sai shi ke bi min.
A halin yanzu za ki kai kamar shekara
nawa da haihuwa kenan Hajiya?
Ina jin zan kai shekara saba’in da
bakwai da haihuwa.
Hajiya maganar iyali fa?
‘Ya’yana goma na haifa kuma ina da
jikoki sittin.
Ko kina wata sana’a ko kasuwanci?
Ni daman can ‘yar kasuwa ce kuma
har yanzu ina sana’ar sai da gwanjo.
Hajiya dama can mahaifinku dan nan
cikin garin Daura ne ko tasowa ku ka
yi daga wani gari?
Asalinmu ba a nan cikin garin Daura
yake ba. Akwai wasu rugage na
Fulani idan ka fita kofar Yamma
kamar za ka tafi Mai Adu’a nan ne
asalin garin mahaifinmu, ana kiran
garin Dumurkol. Mahaifiyarmu kuma
a gidan Sarkin Daura aka haifeta ta
kuma zauna gidan Wazirin Daura
kanen, Sarki Audu a nan ta auri
mahaifinmu kuma sunan ta Zulai.
Mahaifin na ku ya taba rike wata
Sarauta kuwa?
Eh, ya taba. Amma ta Sarkin Fulani
ya yi a kauye Durmukol.
Hajiya ku nawa ne mahaifinku ya
haifa?
Da yake matan mahaifinmu su uku
ne, biyu na kauye mu kuma
mahaifiyarmu na nan cikin gari. Haka
kuma mu ashirin da hudu ne a
gidanmu, amma saura mu biyu muka
rage a raye daga ni sai Buhari. Amma
akwai ‘ya’yansu da jikokinsu duk
muna tare da su.
Yaushe mahaifanku suka rasu?
Na farko mahaifinmu ya rasu tun
muna kanana, amma mahaifyarmu
ta rasu bayan an yi wa Buhari juyin
mulki lokacin da ya yi shugaban kasa
na mulkin soja.
Hajiya wannan fitowa takara ta Janar
Buhari ita ce kusan ta hudu, kuma a
wannan karon Allah ya ba shi nasara
kina ga me ya jawo haka?
Hakuri da kuma jajircewa da kuma
niyyarsa ta alheri da yake da ita ga
kasar nan ita ta jawo hakan. Ka ga
dai har ya rike mukamai daban daban
har ya gama ba ya cin hanci ko
karbar rashawa. Mu kuma ‘yan
uwansa idan ya samu ya ba mu idan
bai samu ba mu yi hakuri. Har ya
gama wadannan ayyuka nasa bai da
gidan kanshi, sai abokai suka yi
masa gida a Kaduna. (Za Mu Ci
Gaba)
Barkada Zuwa shafi mai Albarka. Idan kaga wani abu Bakagane ba kashiga page din ka'aje tambayar ka.
Tuesday, 28 April 2015
Tattaunawa da yayar GMB
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment