Tuesday, 28 April 2015

Tattaunawa: ta biyu da yayar GMB

TATTAUNAWA: (Kashi Na Biyu)
Tun Buhari Na Yaro Yake Da
Kwarjini, Cewar Yayarsa Rakiya
Adamu
Hajiya ya za ki bayyana mana yadda
Janar Buhari ya yi kuruciyarsa, da
kuma yadda ya tafi aikin soja?
Tun lokacin da yake karami yana da
natsuwa da biyayya kuma yana da
kokari kwarai a makaranta. Kuma
yana da farin jini sosai. A lokacin
yana sakandire an taba yin wani taro
a Katsina, shi ya yi na daya har
Turawa suka tafi da shi Ingila, da ya
gama abin da yake a can suka dawo
da shi domin gama sakandire. Bayan
gama sakandire ne ya ce min Rakiya
soja zan tafi, na ce soja za ka tafi, na
ce kar a je a kashe ka Buhari, ya ce ai
ba na kashewa ba ne, a ofis zan
zauna. Bayan shigar sa kuma ya je
yakin Kongo da Biyafara ya kuma
dawo gida lafiya lau.
A lokacin kuruciya ana yi masa wani
lakani bayan sunansa na ainihi?
Akwai wani suna da ake kiransa da
shi ana ce da shi “Hankali”. Suna ne
da yara ke kiransa da shi.
Me ya sa ake kiransa da wannan
suna?
Saboda irin farin jinni da natsuwa da
hangen nesa da Allah ya yi masa tun
a wancan lokacin, ana son shi sosai
manya da yara, kuma da wuya ka ji
ya yi fada da wani yaro, ni dai a
sanina ba shi da abokin fada ko da
yana yaro. Akwai lokacin da
malaminsu (Bature) ya zo makaranta
bai gan shi ba, a lokacin yara sun
sanya mashi allura ya taka yana jinya
a gida. Bature ya ce ina Hankali?
Yara suka ce yana gida, sai aka kira
tsohuwarmu, ta ce yara ne suka
sanya masa allura ya taka, don haka
wannan magana ta makarantar boko
a bar ta, saboda ranta ya baci
matuka, sai aka yi ta ba ta hakuri ta
yadda daga nan ya ci makaranta a
Katsina.
Idan na fahimce ki mahaifansa sun yi
niyyar cire shi daga makarantar
bokon kenan?
Kwarai da gaske saboda abin da ya
faru.
Ya za ki bayyana yadda halayyarsa
take?
Gaskiya halayyarsa na da kyau
kwarai da gaske kuma yana da son
‘yan uwa sosai ga son zumunci. Ko a
lokacin yana makaranta firamare
yana da kokari da hazaka da kuma
maida hankali a karatunsa, shi ya sa
malamai ke son shi kwarai. Hatta
farin jininsa da shi ya taso tun yana
yaro. Kuma mutum ne mai karbar
shawara.
Ko kin samu labarin ya taba yin
shugabanci a makaranta?
Ya taba zama shugaban dalibai
kuma ya yi Ladani a makarantarsu,
ko a lokacin za ka ga ‘yan uwansa
dalibai na ba shi girma, da wuya ka
ga ya shiga harkar da ba a sanya shi
ciki ba. Tunda yayyansa suka rasu
shi ya dauki ragamar shugabanci a
gidanmu, kuma da kwarjini da Allah
ya yi masa tun yana karami kuma ya
rike mu da kyau, komai shi ke yi idan
ya taso musamman wajen karatunsu
da shawarwari tsaye yake.
Lokacin da yake aikin soja ya kuke ji
ganin yana zuwa yake-yake kasashe
daban-daban?
Lokacin yana aikin soja tsakaninmu
da shi kullum sai addu’a, muna
rokonsa Allah ya maido mana shi
gida lafiya. Duk lokacin da zai tafi
irin wadannan yake yake ya kan zo
mana bankwana. Ko a lokacin da za
su yakin Kongo ya zo ya fada mana
sai muka kama kuka kar a je a kashe
ka, kuma ya je lafiya ya dawo lafiya.
Lokacin da ya yi shugaban kasa na
mulki soja yana zuwa ganin gida?
A lokacin da ya yi shugaban kasa ba
shi da gida a Daura na sa na kanshi.
Kuma yana zuwa a duk lokacin da ya
samu dama kuma mahaifiyarmu na
da rai dangi duk sai su taru. Kuma
yana taimaka mana kwarai ko a
lokacin.
Ya ki ka ji lokacin da aka ce Buhari ya
samu nasara wannan zabe na 2015?
Gaskiya na yi matukar farin ciki
wanda bai misaltuwa. Na ji dadi
kwarai kuma na yi godiya ga Allah
madaukakin sarki da ya gwada mani
wannan rana ina raye, kamar yadda
Bahaushe ke cewa mahakurci
mawadaci, yau hakuri ya yi ranarsa.
Kullum ranar duniya mutane na ci
gaba da tururuwa zuwa gidana suna
yi mani murna nasara cin wannan
zabe.
Shin ya na zuwa har nan gidan idan
ya zo Daura ko ke zuwa gidanshi?
Shi ke tako kafarsa har nan gidan duk
lokacin da ya zo. Shi mutum ne mai
girmama na gaba da shi. Kuma hatta
ko wannan lokacin da ya zo zabe sai
da ya zo har nan dakin ya gaishe ni,
kuma ya zauna bisa wannan kujera
muka gaisa.
Wadanne irin ayyuka ki ka fi son ya
maida hankali kansu; ganin ‘yan
Nijeriya na mashi kallon wanda zai
iya kawo gyara?
Samarwa da ‘yan kasa kayayyakin
more rayuwa da tsaro, ayyukan yi ga
matasa, da magance rashawa, dole
‘yan kasa su dan yi hakuri kasar ta
riga ta baci. Amma ina ganin da
yardar Allah zai gyara al’amurra da
dama.
Hajiya menene fatanki?
Fatana ita ce Allah ya ba shi ikon yin
adalci kan wannan shugabanci da ya
samu a kasar nan, kuma ya sanya ya
gama mulkin lafiya.
Daga karshe wane kira za ki yi ga
‘yan kasar nan, musamman wadanda
suka zabe shi da ma wadanda ba su
zabe shi ba?
Na farko ina mika sakon godiya ta
musamman ga al’ummar kasar na
zaben wannan dan uwana da suka yi,
Allah ya saka da alheri kuma insha
Allah ba zai ba su kunya ba. Kiran
kuma da zan yi shi ne su ci gaba da
yi masa addua’a domin samun
nasara a wannan jagoranci.

No comments: