Friday, 4 December 2015

Alfanun Ganawar Buhari Da
Shugaban Kasar Chana
Daga Aliyu Ahmad
A yau ne tawagar shugaban kasa
Muhammadu Buhari take ganawa da
shugaban kasar Chana kasar Afirka
ta Kud game da wani muhimmin
taro.
Maimagana da yawun shugaban
kasa, Femi Adesina ya ce, a
tattaunawar da za a yi, shugabannin
biyu za su cimma yarjejeniya kamar
haka:-
Gina hanyar Jirgin kasa daga Legas
zuwa Kalaba akan kudi Dalar Amurka
biliyan 12 wanda zai samarwa
mutane dubu dari biyu ayyukan yi.
Sai kuma wani layin dogon daga
Kano zuwa Legas akan kudi dala
biliyan takwas da miliyan dari uku.
Za kuma a gina kamfanin samar da
wutan lantarki mai karfin megawat
3,050.
Tawagar shugaba Buharin dai ta
hada da ministocin harkokin
kasashen waje, kasuwanci da zuba
jari da kuma ministan sufuri Rotimi
Amaechi.

No comments: